Jami’an tsaron gwamnatin tarayyar a Amurka, sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla akan masu zanga-zanga da suka taru a wajen ginin kotun gwamnati kasar da ke birnin Portland a jihar Oregon.
Zanga-zangar ta jiya Laraba, ita ce rana ta 56 da masu boren suke fita a jere domin nuna fushinsu kan zargin da suke yi wa ‘yan sanda na cin zali, da nuna wariyar launin fata da kuma girke jami’an tsaron gwamnatin tarayya da aka yi a birnin na Portland.
A lokacin da wannan lamari ke faruwa, Magajin Garin birnin na Portland Ted Wheeler na tsaye a kusa da wata katanga da ke gefen kotun yayin da jami’an tsaron suke jefa barkonon tsohuwar akan masu zanga zangar.
Tun gabanin aukuwar wannan lamari, Magajin Garin ya isa inda ake zanga-zangar ya kuma nuna goyon bayansa ga masu boren, amma da yawa daga cikin su, sun yi ta masa ihun nuna rashin gamsuwa.
Facebook Forum