‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da maida murtani akan karin albashin da gwamnatin Najeriya ta amince da shi a rundunar tsaron ‘yan sanda, abinda wasu ke ganin cewa karin ba zai taimaka wajen inganta harkokin tsaro da kuma canza ra’ayin ‘yan sanda gameda cin hanci da rashawa ba, wasu kuma na gani matakin zai taimaka gaya wajen inganta rayuwar ‘yan sandan da kuma tabbatar da tsaro.
‘Yan sandan dai sun yaba da wannan matakin. Wani dan sanda da ya so a sakaya sunansa ya ce zai taimaka ainun wajen kara masu kwazo wajen aiki saboda sun dade suna yin korafi akan a yi masu karin albashi. Fatansa shine su gani a kasa.
Shi kuma malam isa Mani, cewa yayi malaman makaranta ya kamata a karawa albashi ba ‘yan sanda ba saboda ko me aka kara masu ba zasu bar cin hanci da rashawa ba, duk da cewa gwamnatin Najeriya na gani batun tsaro zai inganta.
Shekaru kusan 11 da suka gabata ne gwamnatin marigayi Alhaji Ummaru Musa ‘Yar Adua ta yiwa ‘yan sada karin albashi don zaburar da su wajen tunkarar batun tsaro. Yanzu dai abin jira a gani shine ko wannan karin da aka yi zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da kawas da cin hanci da rashawa da wasu ke gani yayi katutu a tsakanin wasu ‘yan sandan na Najeriya.
Ga karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin
Facebook Forum