Wasu masu gadi ma Majalisar Dinkin Duniya su hudu sun samu raunuka sanadiyyar tashin wani bam din da aka dana a wata mota daura da ginin da su ke ciki a birnin Mogadishu, a cewar jami'ai a Somaliya.
Dukkan wadanda abin ya rutsa da su Somaliya ne. Daya daga cikinsu, wanda shi ne shugaban masu aikin gadi na yankin, ya samu raunuka masu yawa, a cewar jami'an. Kafar labaran Reuters ta ce kungiyar mayakan nan ta al-Shabab ta dau alhakin kai harin.
Fashewar ta auku ne a wani dan garejin da ke dab da ginin shirin kawo cigaba na Majalisar Dinkin Duniya da ke babban birnin kasar.
Wani jami'in leken asiri wanda ya je wurin da abin ya auku ya gaya ma Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka cewa an dana bam din ne cikin motar da ke garejin, wanda hukumar UNDP ke amfani da shi. Motar ta shiga garejin ne da safiyar yau Laraba, a cewar majiyoyi.
"Fitar direban daga motar ke da wuya sai kawai fashewar ta auku," a cewar jami'in, wanda ya bukaci a sakaya sunansa.
An kama mutane 9 dangane da wannan fashewar.