Wasu rahotannin masu dumi-dumi daga jihar Taraba, na nuni da cewar an samu kama wata yarinya ‘yar makarantar kwalegin gwamnatin tarayya ta mata a garin Jalingo dauke da gurneti. Wannan dalibar dai ta dawo makaranta ne daga hutun sabuwar shekara, wanda ayayin da hukumomin makarantar ke kokarin bincike kayan dalibai don tabbatar da cewar kowace daliba bata dauke da wasu muggan kaya.
A cikin wannan binciken ne akasamu ganin wadannan gurnetin a cikin kayanta, wanda hukumomin makarantar sun hannunta ta ga jami’an tsaro don guda nar da bincike. Labarai dai na nuni da cewar wannan yarinyar diyar wani tsohon soja ne wanda hukumomi basu bayyanar da kowanene babanta ba. Ita dai wannan yarinya me suna Blesin, yar garin Numan ce. Tabakin kakakin rundunar ‘yansanda a jihar Taraba ASP. Joseph Kuji, ya bayyanar da cewar har sun tura jami’an kwance boma bomai don su kwance wannan bom in, kuma su aiwatar da bincike yadda yakamata.
A cewar Dr. Abdullahi Bawa Wase, yace mutane su mai da hankalin dangane da al’amurran da ke gudana a yankunansu, yace duk wani abu da mutane suka gani wanda bai gamsar da suba to su hanzarta sanar ma hukumomi, da suke kusa suku ma sanarma jami’an gwamnati domin daukan matakan gaggawa. Yace al’umah su guji taba wani abu da basu san ko menene ba, idan har basu suka ajiye shiba, Sannan su hanzarta sanar da hukumomi don daukan matakin da ya dace a lokacin da yakamata.