Dimbin ma’aikata maza da mata ne suka hallara a harabar ta ma’aikatar Ministan kwadago a yau Litinin 24 ga watan Agusta wuni na farko kenan na yajin aikin kwanaki 3 da suka tsunduma da nufin tayar da gwamnatin Nijer daga barci akan maganar soma basu wasu kudaden alawus din da aka yi alkawalin soma bayarwa a karkashin wata dokar da aka saka wa hannu a shekarar 2014. Malan Mahamadou Ali China na daga cikin jagororin kananan ma’aikata.
Yanayin tsadar rayuwar dake kara ta’azzara a kullayaumin a nan Nijer wani al’amari ne da kananan ma’aikata ke ganin ya kai matsayin da mahukunta za su ankara da mawuyacin halin da irin wadanan ma’aikata ke ciki..
To sai dai gwamnati a ta bakin darektan ofishin Ministan kwadago Ibrahim Yacouba Adamou na cewa kananan ma’aikatan sun nuna gajen hakuri domin tuni takardu suka isa ma’aikatar kudi.
A kalla kananan ma’aikata kusan 8000 ne suka jingine aiki a wunin farko na wannan yaji aiki da aka bayyana cewa ya yi tasiri a nan Yamai da sauran yankunan kasa to amma ganawar da aka yi a tsakanin jami’an Ma’aikatar Kwadago da jagororin masu wannan gwagwarmaya an umurci kananan ma’aikata su koma kan aiki sakamakon gamsuwa ba bayanan da suka ce sun ji daga bangaren hukumomi.
Saurari cikakken rahoton Sule Barma a sauti:
Facebook Forum