Shugaban Amurka Donald Trump ya ce lokaci ya yi da za a sake bude harkokin tattalin arzikin kasar, ko da hakan na nufin mutane da yawa za su kamu da cutar coronavirus.
“Jama’ar kasarmu gwarzaye ne,” in ji Shugaban, yayin wata ganawa da manema labarai a jihar Arizona.
Ya kara da cewa, “ko lamarin zai shafi jama’a sosai? Eh, amma dole ne mu bude harkokin tattalin arzikinmu."
A cedar Trump, “za a samu karin mace-mace,” sannan ya kuma yi hasashen cewa annobar coronavirus za ta wuce ko da magani ko ba magani.”
Trump dai ya kai ziyara ne a babban kamfanin sarrafa kayayyakin Honeywell da ke garin Phoenix kamar yadda gidan talabijin din ABC News ya nuna a wata hira da ya yi da Trump,
An ba kamfanin na Honeywell kwangilar dala miliyan 27.4 don sarrafa takunkumin rufe hanci da baki na N95 guda miliyan 38 da za a samar cikin wata 6.
A hallin da ake ciki, Amurka na da dadin mace-mace sama da 69,000 sanadiyyar cutar coronavirus, kusan fiye da kowacce kasa, ga kuma hasashen da ke cewa mutane fiye da dubu 134 za su mutu daga nan zuwa farkon watan Agusta.
Facebook Forum