WASHINGTON —

Hatsarin ya faru ne ranar Laraba inda aka tabbatar da cewa mutum 22 sun tsira da rayukansu, yayin da ake ci gaba da aikin ceto ko neman sauran mutanen da suka bata.

An gano gawar wata yarinya daya a cewar shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kebbi, Sani Dododo.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun nutsewar jiragen ruwa kuma ana samun asarar rayuka ba.

Ko a watanni baya an samu irin haka a garin Jega jihar ta Kebbi da kuma Goronyo da Shagari a jihar Sokoto, inda masu lura da al'amura irin Bello Daudun Badah na ganin akwai sakacin hukuma.

Sai dai shugaban hukumar bayar da agajin gaugawa a jihar Kebbi Sani Dododo ya ce, hukumomi na bakin kokarinsu kawai mutane ne ba su bin ka'idoji.

Bisa la'akkari da yadda ake samun asarar rayukan ‘yan Najeriya ta hanyoyi daban-daban, masana na ganin cewa da jama'a da hukumomi suna bin ka'idojin tafiyar da lamurra da watakila za'a iya kaucewa faruwar wasu daga ciki.

Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.

Jirgin Ruwa Ya Nutse Da Mutum160 a Jihar Kebbi- 3'22"

Yadda Jirgin Ruwa Ya Nutse Da Sama Da Mutum 100 A Jihar Kebbin Najeriya

Wani jirgin ruwa dauke da mutum kimanin 160 ya nutse a garin Warrah dake karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi, lamarin da ya zuwa yanzu ba a san adadin mutanen da suka rasu ba.