Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwangilar Gina Matatar Mai Tsakanin Nijar Da Canada Ya Bar Baya Da Kura


Wata Matatar Mai A Legas
Wata Matatar Mai A Legas

Kungiyar Transparency International ta gargadi mahukuntan Jamhuriyar Nijar da su soke yarjejeniyar ayyukan gina matatar da suka cimma da kamfanin Zimar na kasar Canada bayan da ta ce bincikenta ya gano cewa kamfanin Zimar na daga cikin irin kamfanonin da ke kewaye wa hanyoyin biyan haraji

A sanarwar da ta fitar Kungiyar ta ce akwai bukatar hukumomi su gudanar da bincike don gano abubuwan da ke boye bayan wannan kwangila da ta ke zargin ba za a rasa alamomin cin hanci tattare da ita ba.

Kwangilar akalla billion 600 na kudaden CFA ne aka sanar cewa an bayar a karkashin yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin gwamantin Nijar da Zimar Canada domin gina matatar da za a rinka tace ganguna 100,000 a kowace shekara hade da wani katafaren dakin binciken kimiyar man fetur a Dosso.

Sai dai Transaparency tace a bayanan da ta tattara daga 'yan Nijar mazauna Canada da ma wadanda aka jiyo daga kafafen kasar na nunin Zimar ba shi da kwarewar gudanar da irin wannan gagarumin aiki saboda haka kungiyar ta shawarci gwamantin Nijar ta soke wannan kwangila, a cewar shugaban kungiyar Maman Wada a sanarwar da suka fitar.

Haka kuma Zimar Canada na daga cikin kamfanonin da ake zargi da kewaye hanyoyin biyan haraji inji Transaparency abinda ke zama manuniyar dake fayyace alamun cin hanci da karbar rashawa a harkokinta.

Muryar Amurka ta tuntubi sashen labarai a ofishin ministan man fetur domin jin martanin hukumomi kan wadanan kiraye-kiraye na kungiyar Transparency, to amma an bukaci mu bada lokaci a sanar da ministan daga bisani za a waiwaye mu, sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a tuntube mu ba.

Koda yake wani dan fafutika Mahamadou Tchiroma Aissami wanda shi ma ke nuna rashin gamsuwa da kwarewar Zimar yace akwai alamun korafin na jama’a ya shiga kunnen da ya dace.

A watan Oktoban da ya gabata ne ministan tsaron kasa Janar Salifou Mody amadadin firaiminista ya saka hannu kan takardun yarjejeniya da Zimar Canada wacce a karkashinta gwamnatin Nijar ta aminta da kamfanin a matsayin wanda zai gudanar da ayyukan gina wannan matata.

Koda yake ajawabinsa na waccan lokaci Ministan ya tabbatar da cewa Zimar amintacce ne ‘yan kasa na da tababa game da wannan kamfani da ke ci gaba da zama abin mahawwara a kafafen sada zumunta.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Kungiyar Transparency Ta Yi Kira A Soke Yarjejeniyar Kwangilar Gina Matatar Mai Tsakanin Nijar Da Canada.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG