Cibiyar binciken magunguna ta kasa a Najeriya NIMR, za ta fara yin gwajin cutar coronavirus kyauta.
Shugaban cibiyar, Farfesa Babatunde Lawal Salako ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce za a fara gwajin ne a ranar Litinin mai zuwa a ofishin cibiyar da ke Yaba a jihar Legas.
Sanarwar wacce ya wallafa a shafinsa a karshen makon nan ta kara da cewa, “wadanda suka fi bukatar gwajin za a fi ba fifiko, musamman in sun tabbatar cewa sun yi mu’amulla da wani da ke dauke da cutar.”
Jihar Legas dai ita ta fi kowacce jiha yawan masu fama da cutar a Najeriya, a nan ne kuma cutar ta fara bulla bayan da wani dan kasar Italiya ya shiga da ita a karshen watan Fabrairu.
Ya zuwa ranar Juma'ar da ta gabata, hukumar NCDC mai kare yaduwar cututtukan a kasar ta ce mutum 52 ke dauke da cutar a Legas kadai.
Facebook Forum