Amma hukumar EFCC na bayyana kwararan hujjoji da zasu sa a hanashi beli domin zargin da ake yi masa da yin almundahana da samada miliyan dari shida da kuma sama da dala biliyan biyu.
Tun farko EFCC ta gabatar da mutane biyar ciki ko har da shugaban gidan talibijan na AIT Raymond Dokpesi. Tace tuhumar da ake yiwa mutanen zata cigaba da gudana har sai an hukunta wadanda ake zargi ba kamar yadda ake yi a can baya ba inda ake yin dogon turanci da bata lokaci.
Kakakin hukumaar EFCC yace zasu ba kotu damar kawar da kokwanton da su keyi. Amma ya karfafa yiwuwar samun kotuna na musamman da zata yi shari'ar wanda ake tuhuma da almundahana saboda kotun na yanzu suna da dimbin kararraki a gabansa lamarin dake sa ana daukan dogon lokaci kafin a gama shari'a daya..
A wani hannun kuma lauyan Raymond Dokpesi yana murnar samar masa beli abun da ya saura yanzu shi ne cike sharudan da kotu ta gindiya masa.
Dokpesi da ake tuhuma da karbar fiye da nera biliyan biyu yace ya yi anfani da kudaden ne ta hanyar tallata harkokin kemfen din tsohon shugaban kasa mai makon sayen makamai.
Lauyansa yace koda ma an sami Dokpesi da laifi baiwuce a bashi daurin shekara bakwai ba saboda haka yana mamakin abun da ya sa aka samu tsaikon bada belinsa..Haka kuma lauyan yace shari'ar zata kwashe wajen watanni goma sha takwas ana ta tafka muhawara. Yace yana fata EFCC ba zata zo daga baya ta kama Dokpesin ba da wata sabuwar tuhumar.
Ga karin bayani.