Idan dai ba'a manta ba Shugaban kasa ya bada umurnin a kama Kanar Dasuki tare da mutanen da suke da hannu wajen bada kwangilolin bogi na biliyoyin nairori da daloli na sayen makamai.
Sambo Dasuki wanda ya samu beli daga wata kotu makon jiya ya kasa fitowa daga gidansa domin ya san jami'an tsaro zasu yi awan gaba dashi.
Yanzu mutane sun soma tofa albarkacin bakinsu akan binciken da ya bankado almundahana ta biliyoyin nera da miliyoyin dala.
Anas Dan Nayaba wani mai rajin dimokradiya yace bincike nada kyau idan bisa ga gaskiya aka yi shi. Shugaban kasa na yanzu yana kishin kasar. Babu maganar kabilanci da shi ko bangaranci.Yace bata yiwuwa a yi mulki wasu mutane kuma su fi gwamnati kudi saboda zasu iya kawowa gwamnatin baraka. Dole ne mutanen su mayarda kudaden asusun gwamnati idan har ana son a samu zaman lafiya.
A wata sanarwar da ya fitar Kanar Sambo Dasuki ya zargi gwamnatin Buhari da neman lankaya masa laifin da bai aikata ba.
Ga karin bayani.