A cewar kungiyar kwadago ta duniya- ILO, miliyoyin mutane ne ke fama da rashin lafiya ko kuma ace su na jin rauni a wurin aiki a kowace shekara, kuma kusan ma’aikata miliyan 3 a duniya na mutuwa sakamakon hatsari a wajen aiki ko kuma sanadiyyar cututtuka.