Rahoton da ‘yan kungiyar masu bincike daha kasar Slovenia suka wallafa jiya laraba ya fito lokaci daya da wani sharhi daga wasu kwararrun jami’an kiwon lafiyar Amurka da ke goyon bayan abinda ‘yan kungiyar ta Slovenia suka rubuta.
Farfesa Tatjana Avsic Zupanc, wanda ya jagoranci binciken a cibiyar kiwon lafiyar jami’ar Ljubljana (Lubliyana), ya fadawa kamfanin dillanci labaran Reuters cewa binciken da kwararrun suka yi zai iya bada hujjoji masu karfi da ke nuna cewa cututtukan jarirai da ake haihuwa da su, masu alaka da cutar Zika, ta yiwu suna faruwa ne idan kwayar cutar ta rubanya a kwakwalwa.
An gudanar da binciken ne akn wata mace mai juna biyu da ke dauke da cutar ta zika, amma ta zubar da shi bayan da gwajin juna biyu na na’urar ya nuna cewa dan da take dauke da shi ya nuna alamun wasu matsaloli tattare da shi.
Binciken ya ce matar ba ta da tarihin wadannan matsalolin a danginta kuma bata taba kamuwa da wasu kwayoyin cuta da za su iya haddasa wannan matsalar ba.