Kila kwamitin sulhun MDD ya yi taron gaggawa a yau Laraba a asirce a kan gwajin makami mai lizami da Korea ta Arewa ta kaddamar a baya bayan nan.
Amurka ce ta bukaci shirya wannan zaman gaggawar. Masu pashin baki akan harkokin sojin Amurka sun yi zaton Korea ta arewa tayi gwajin makami mai linzami da ka iya zuwa wata nahiya da ka iya zuwa Alaska.
Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Pyongyang takunkumai da dama, to amma kila basu shawo kan Korea ta arewa ta yi watsi da shirinta na makaman nukiliya.
Wannan gwajin na baya bayan nan ya tada hankalin babban kawara Korea ta Arewar, China, wacce a halin yanzu majalisar tsaronta ke ganawa a fadar shugaban kasa. Da alama dai China bata cimma nasara ba wurin baiwa Korea ta Arewa shawara ta daina gudanar da gwaje gwajen ba.
Facebook Forum