Shugaba Muhammad Buhari ya bada umurnin a gudanar da cikakken bincike akan sakataren gwamnatinsa David Lawal Babachir dangane da badakalar da ta kunno kai akan kwangilar taimakawa 'yan gudun hijira a arewa maso gabas wadanda yakin Boko Haram ya dagargazasu.
Haka ma shugaban ya dakatar da babban daraktan leken asirin hukumar kasa da kasa ta Najeriya Ambassador Ayo Oke wanda ake zargin cewa wai kudaden hukumarsa ne aka samu a wani gida a birnin Legas. Kudin sun haura Naira biliyan dubu goma sha biyar.
Wadannan mutanen biyu an dakatar dasu daga bakin aikinsu nan take har sai an gama bincike.
Malam Garba Shehu kakakin fadar Shugaba Buhari yana mai cewa cikin abubuwan da Shugaba Buhari yake son a gano masa shin kudaden da aka kama wanene ya bada umurnin a fitar dasu daga asusun gwamnati. Ta yaya ma aka fitar dasu. Wanene aka ba kudin kuma yaya aka yi aka samu kudin a gidan wani.
Kwamitin da aka kafa zai binciki wadannan lamura biyu, wato batun sakataren gwamnati da ita hukumar NIA. Shugaban kasa na bukatar rahoton kwamiti din cikin kwanaki goma sha hudu. Bayan rahoton ne zai dauki matakan da suka dace.
Sai dai shugabar kungiyar 'yanto hakkokin 'yan Najeriya kuma kusa a jam'iyyar APC Hajiya Naja'atu Muhammad tace tana son a dauki mataki akan mutanen dake kusa da gwamnati da ake zarginsu da yin sama da fadi da dukiyar jama'a baicin wadannan biyun. Tana mai cewa wannan matakin da ya kamata an daukeshi tuntuni.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum