Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SERAP, CISLAC Sun Bukaci Majalisar Dokokin Najeriya Ta Yi Watsi Da Shirin Sayen Motocin Alfarma 465


Shugaban Kungiyar CISLAC, Awwal Ibrahim Musa Rafsanjani
Shugaban Kungiyar CISLAC, Awwal Ibrahim Musa Rafsanjani

A Najeriya, wasu manyan kungiyoyi biyu sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta janye shirin yin amfani da sama da dala miliyan 56 don siya wa ‘yan majalisar dokokin da wasu jami’ai motocin alfarma guda 465 masu kariyar harsashi.

WASHINGTON, DC - Kafofin yada labaran Najeriya sun ce shirin ya kunshi kusan dala miliyan 88 don sayen sabbin ‘yan majalisar. Shugabannin kungiyar sa ido a kan harkokin da suka shafi majalisun dokoki ta CISLAC da kungiyar SERAP mai sa ido kan tattalin arzikin al’umma a Najeriya, sun ce wannan kudurin tamkar nuna halin ko in kula ne ga yanayin kuncin da talakawan Najeriya ke ciki.

Kungiyar SERAP ta kuma ba hukumomin wa'adin mako guda su yi watsi da shirin.

Kungiyoyin biyu sun kira masu goyon bayan shirin marasa kishin kasa musamman a daidai lokacin da ake fuskantar tashin farashin man fetur, da hauhawar farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi.

A wata hira da ma’aikacin Muryar Amurka Peter Clottey, Auwal Musa Rafsanjani, babban daraktan kungiyar CISLAC, ya fadi cewa ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ba a sayo sabbin motocin na alfarma ba don ministoci da wasu jami’an gwamnati.

Ya kara da cewa a halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, sayen wadannan motocin bai da muhimmanci a yanzu, duba da cewa ranto kudin za'a yi.

"Kamata ya yi a yi amfani da kudin don sassauta kuncin da ‘yan kasar ke ciki" a cewar Rafsanjani.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG