Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Litar Mai Ya Koma N617, ‘Yan Najeriya Na Neman Mafita


Gidan mai a Abuja
Gidan mai a Abuja

A yau talata ne al’ummar Najeriya musamman a manyan birane ciki har da Abuja, Legas, Kano, Kaduna da dai sauransu, suka wayi gari da tashin farashin man fetur daga naira 537 zuwa naira 617 ko wace lita.

Duk da tsananin rayuwa da ‘yan Najeriya suka yi korafin shiga tun bayan janye tallafin man fetur a karshen watan Mayu da sabuwar gwamnatin ta yi, a yau ‘yan kasar sun wayi gari da kari a farashin kowacce litar man fetur zuwa naira 617 a wasu gidajen man kamfanin man fetur na kasar wato NNPCL wanda ya tashi daga Naira 537 lamarin da tuni ‘yan kasar suka fara tir da shi.

Wata ma'aikaciyar wani gidan mai a birnin Lagos, bayan da aka cire tallafin mai.
Wata ma'aikaciyar wani gidan mai a birnin Lagos, bayan da aka cire tallafin mai.

Wakiliyarmu ta lura da gidajen man kamfanin NNPCL a birnin tarayya Abuja na sayarwa a kan naira 617, AYM shafa a kan naira 550 sai gidan man Azman a kan naira 620 kamar yadda wasu ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu suka tabbatar, inda suka bayyana cewa duk wani sauyi na farashi a gidajen man kamfanin NNPCL alama ce ta tashin farashin man ga kowa.

Layin gidan mai a Abuja
Layin gidan mai a Abuja

Tuni dai ‘yan Najeriya daga sassan kasar daban-daban suka fara nuna rashin jin dadinsu a kan yadda wannan matakin zai kara jefa mutane cikin karin tsananin rayuwa musamman ma ganin irin tsananin da aka shiga tun bayan janye tallafin man fetur da sabuwar gwamnatin Tinubu ta yi a karshen watan Mayu.

Malam Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu a kafoffin sada zumunta kwararre ne a fannin yada labarai da sadarwar kuma dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar PRP a zaben watan Maris daya gabata, ya ce hauhawar farashi musamman ma na man fetur abu ne mai tada hankali.

Akan haka ya bukaci gwamnati "ta tsaya ta yi nazari ta dauki matakan gaggawa na kawo wa talaka sauki tun ana zaune lafiya kafin abu ya rikide zuwa masifar da ba za ta iya karewa ba."

Shi ma masanin tattalin arziki, Mal. Kasim Garba Kurfi cewa ya yi karin da aka gani ba abin mamaki ba ne saboda idan farashin mai na tashi a kasuwannin duniya dole ne a rika ganin kari a cikin gida.

Ya kara da cewa kamata ya yi gwamnati ta dauki matakan da suka dace doń sassauta ma al’umma.

Tun bayan kowamawa tsarin mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999 ne, Najeriya, kasa ta biyu a fannin samar da mai a nahiyar Afrika bayan kasar Angola, ta fada cikin cece-kuce game da tsarin tallafin man fetur kafin cire shi a watan Mayun shekarar nan.

An fara aiwatar da manufar a matsayin wani mataki na tsawon watanni shida don daidaita farashin man fetur a waccan lokacin gyaran matatun man cikin gida, lamarin da ya ci gaba da dawwama tsawon shekaru da dama duk da cewa an dan cire shi na wani dan gajeren lokaci a baya.

Tallafin dai ya kasance makami mai bangare biyu, wanda ya baiwa ‘yan kasar da dama agaji baya ga cewa ana zargin yana ba da dama ga masu aikata cin hanci da rashawa da tabarbarewar tattalin arziki a kasar.

Idan Ana iya tunawa a ranar 29 ga watan Maris ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur lamarin da tuni ya jefa ‘yan Najeriya cikin matsin rayuwa in ji masana.

Duk kokarin ji ta bakin hukumar NMDPRA mai kula da dokokin fannin albarkatun man fetur da iskar gas ta Najeriya, kamfanin NNPCL da kungiyar dilalan man fetur ta IPMAN ta wayar salula a yayin hada wannan rahoton dai ya ci tura.

Saurari rahoto a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG