Shuwagabannin mata na kasar Sudan ta Kudu, sun bukaci shugaban kasar da ya baiwa mata kashi 35 daga cikin dari kamar yadda yarjejeniyar samun zaman lafiya a kasar ta tanada.
Ranar Talata shugaban kasar Salva Kiir, ya nada kwamiti mai mutane 10 da aka dorawa nauyin fara shirin kafa gwamnatin wucin gadi. Mace daya kurum ya nada cikin kwamitin mai mutane 10.
Mary Ayen Majok, mamba a kwamitin ta bayyana ma VOA jiya Laraba cewar, ba suji dadin gwamnatin, bata baiwa mata kason da yarjejeniyar ta tanada ba.
Ba’a kaddamar da wannan shirin na baiwa mata kashi 35 cikin 100 ba a cewar Majok. Gare mu kuwa bamu ji dadin hakan ba, don hakan na nufin bangarorin basu mutunta ka’idodin yarjejeniyar da aka cimma a Addis Ababa ba.
Facebook Forum