Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Ma'aikatan Jami'o'i Na SSANU Da NASU Sun Tsunduma Yajin Aiki


SSANU/NASU
SSANU/NASU

Kungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya (SSANU) da takwararta ta Ma'aikatan Da Ba Malamai ba (NASU) sun fara wani yajin aikin gamagari akan abinda suka bayyana da rashin adalci da nuna bambanci wajen biyan bashin albashi daga bangaren gwamnatin tarayya.

WASHINGTON DC - A cewar Shugaban Kungiyar ssanu, Muhammad Ibrahim, a wani shirin tashar talabijin ta Channels na sassafe mai suna "Morning Brief" na yau Litinin, "tabbas an riga an fara wannan yajin aiki".

Tun daga yau Litinin, daukacin mambobinmu dake sashen tattara bayanai dana harkokin kudi dana ayyuka da gyare-gyare da tsaro harma dana kula da harkokin dalibai sun janye ayyukansu kuma babu abunda zai sake faruwa a bangaren gudanarwar jami'o'in gwamnatin Najeriya nan da mako guda har sai gwamnatin tayi abinda ya dace".

Ya kuma koka da cewar, babu wani jami'in gwamnatin daya tuntubesu duk da cewa an samu wasu da suka yi hakan amma ba'a hukumance ba saidai yace tabbacin da suka bayar ba wanda za'a iya dogaro akansa ba ne wajen samun biyan bukata.

Shugaban kungiyar ta SSANU yace "akwai masu yiwa gwamnatin zagon kasa" inda yace yana mamakin yadda shugaban kasa bola tinubu zai bada umarni akan biyan mambobin kungiyoyin ma'aikatan jami'o'i bashin albashin da suke bi tun daga shekarar 2022 amma wasu jami'an gwamnatin suyi burus da hakan.

Ya kara da cewar, har yanzu Ministar Kwadago, Nkruka Onyejeocha bata tuntubesu ba duk kuwa da wa'adin mako guda da kungiyoyin suka bayar a Litinin din data gabata, abinda yace ya sabawa dabi'ar tsohon ministan kwadago, Chris Ngige na yin martani cikin sauri.

Muhammad Ibrahim ya cigaba da cewar, matukar gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatunsu bayan cikar wa'adin mako guda na yajin aikin gargadin daya soma daga yau Litinin, “kungiyoyinmu zasu sake zama domin daukar mataki na gaba’.

A litinin din data gabata, 11 ga watan Maris din da muke ciki, kungiyoyin Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya na ssanu da nasu suka yi barazanar garkame dakunan kwanan dalibai tare da katse wutar lantarki a ilahrin jami'o'in kasar nan matukar gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatunsu kan nan da yau 18 ga watan Maris din da muke ciki.

Shin yaya wannan yajin aikin zai shafi daliban jami’o’in kasar, daliba a jami’ar Maiduguri, Fatima Kabu, ta ce duk da cewa ba’a kai ga rufe kofoffin ajujuwa ba amma wasu malamai, masu kasuwanci a cikin jam’iar ta su basu fito ba.

Idan aka fada cikin yajin aikin gamagari kamar wannan, shuwagabannin kungiyoyin na bibiyan mambobinsu a fadin kasar don ganin an mutunta umarnin aiwatar da yajin aikin, kuma a yanzu rahotanni daga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, sun yi nuni da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka yadda aka saba gani.

A wani bangare, a yanayin da ake ciki, ana ci gaba da gudanar da jarabawa a jami’ar Bayero dake Kano kamar yadda Shugaban Sashen Sadarwa da Koyan Aikin Jarida na jami’ar, Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi ya tabattar.

Daga birnin tarayyar Najeriya masani a fannin ilimi kuma babban malami a fannin koyarda siyasar tattalin arziki a jami’ar Abuja, Dakta Faruk BB Faruk, yace sai bayan ‘yan kwanaki ake ganin tasirin yajin aikin kungiyoyin nan 3 a kasa kuma yana mai nuna goyon baya ga a biya su hakkinsu.

Duk kokarin ji ta bakin bangaren gwamnati wato babba da karamin ministan ilimi ya ci tura domin basu amsa kira ko sakonnin kar ta kwana na text da muka tura musu ba.

Tun ba yau ba ake zargin gwamnatin tarayya na nuna banbance-banbance ga kungiyoyin malaman jami’o’in 4 wato ASUU, NASU, SSANU da NAAT inda ake ganin an fi fifita bangaren masu koyarwa a kan saura 3 lamarin da a baya gwamnati ta sha musantawa.

A saurari cikakken rahoton Halima Abdulra'uf:

Kin Biyan Bukatun Mu Ya Sa Muka Tsunduma Yajin Aiki - SSANU, NASU, NAAT
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG