Kin Biyan Bukatun Mu Ya Sa Muka Tsunduma Yajin Aiki - SSANU, NASU, NAAT
A yayin da mambobin kungiyoyin manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya wato SSANU, da na ma’aikatan da ba na koyarwa ba wato NASU da NAAT suka fara yajin aikin gargadi a fadin kasar, wasu jami’o’in sun bi umarni ba su je aiki ba a wani bangare kuma ayyukan sun tsaya cir a wasu jami’o’in kasar.