A yau talata wasu kungiyoyin kwadago daga kasashen Afirka ta Yamma suka fara gudanar da taron kwanaki 3 a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, da nufin tattauna matsalar tsaron da ta addabi al’ummomin wannan yanki, da kuma yadda za su bullo da shawarwarin da suke ganin zai taimakawa gwamnatoci wajen neman mafita.
Ganin yadda matsalar tsaro ke barazanar hanawa gwamnatoci da ma’aikata aiki, a yankunan da ke fama da hare haren ta’addanci a kasashe da dama na Afirka ta Yamma, ya sa kungiyar kwadago ta CDTN shirya wannan taro.
Muhimmancin wannan maudu’I ya sa kungiyar kwadago ta Najeriya aiko da tawaga ta musamman domin halartar wannan taro a karskashin jagorancin mataimakin shugabanta Dr. Nasir Idris.
Da yake jawabi a yayin bukin bude taron ministan kwadagon jamhuriyar Nijar Ben Omar Mohamed ya yaba da wannan yunkuri domin a cewarsa halin da ake ciki a yau a yankunan karkara ya kai matsayin da kungiyoyi kwadago zasu yiwa hukumomi rakiya domin neman mafita.
A yammacin alhamis mai zuwa ne za a kammala wannan taro da aka bayyyana cewa zai fito da wata sanarwa mai kumshe da kiraye kiraye zuwa ga kasashen duniya akan bukatar su dubi Yankin Afirka ta Yamma da idon rahama.
A saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Facebook Forum