Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Na Shirin Tafiya Yajin Aiki Kan Albashi a Najeriya


ABUJA: 'Yan kungiyar kwadago masu zanga zanga
ABUJA: 'Yan kungiyar kwadago masu zanga zanga

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta sanya ma’aikata a shirin tafiya yajin aiki a Talatar nan matukar zuwa karshen wunin yau Litinin gwamnatin Najeriya ba ta cimma matsayar karin mafi karancin albashi Naira dubu 30 ba.

Wannan mataki ya biyo bayan rashin cimma matsaya tsakanin wakilan kungiyar kwadagon da gwamnatin Najeriya, da ta kafe kan karin Naira dubu 4500 wato kudin su kai Naira dubu 22,500 daga dubu 18.

Jami’in kungiyar kwadagon Komrad Nuhu Toro, ya ce matukar ba Naira dubu 30 a ka kai mafi karancin albashin ba, yajin aiki mai tsanani na nan tafe.

Rahotanni sun baiyana cewa sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha, na baiyana cewa zuwa Litinin din nan za a kammala rahoto tsakanin sassa uku na yarjejeniyar don tsayar da mafi karancin albashin.

Saleh Bakoro Damaturu, talaka ne a arewacin Najeriya da ke fargabar yajin aikin ka iya kawo cikas ga masu karamin karfi.

In za a tuna a kwanakin baya kungiyar kwadagon ta gudanar zanga-zangar gargadi don matsawa gwamnati lamba ta kara albashi.

Domin karin bayani saurari rahotan Saleh Shehu Ashaka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG