Kungiyoyin Alkalai, lauyoyi da ta akawun kotuna a Jamhuriyar Nijer sun kafa wata hadaka mai lakabin CCAJ da nufin gwagwarmayar ganin hukumomin kasar sun damkawa kotu rahoton binciken da ya bankado handamar dubban miliyoyin cfa a ofishin ministan tsaron kasa, don ganin an soma shari’ar mutanen da ake zargi.
A sanarwar hadin guiwar da suka fitar, masu ruwa da tsaki a sha’anin shari’a, wadanda suka taru a farfajiyar kotun Tribunal de Grande Instance dake Yamai, sanye da bakaken rigunan aiki, sun yi tuni game da wasu mahimman tanade - tanaden kundin tsarin Mulki da ma dokokin kasa da kasa.
Me Boubacar Oumarou, shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa ya ce, tafarkin damokaradiya wani abu ne da ya rarraba tsarin gudanar da sha’anin Mulki a tsakanin rassan dake da wannan hurumi, saboda haka ma’aikatar shari’a ce kadai ke da ikon tantance gaskiyar zargi ko akasin haka, sannan dukkanin ‘yan kasa na da matsayi guda a gaban doka, haka kuma shari’a zaman kanta take.
Mai shari’a Zakari Yaou Mahamadou, shine jigon kungiyar alkalai ta SAMAN, ya ce, dole ne gwamnatin Nijer ta gaggauta gabatar wa alkalai rahoton binciken.
Biliyan 1700 na kudaden cfa ne aka bayyana cewa an zuba a ma’aikatar tsaro domin tunkarar matsalar ta’addanci da kasar ke fuskanta, sai dai bincike ya gano an yi rub da ciki akan wani bangare na wadanan kudade, lamarin da ya sa ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan kasa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Facebook Forum