Wasu Kungiyoyin Fulani sun yi barazanar kai Gwamnatin Tarraya Najeriya kotu, kan ci gaba da rike shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore Abdullahi Bello Badejo, bayan kwanaki 10 da kama shi da suka yi.
Kungiyoyin Fulani na FAYAN da FANAM sun koka ne a wata sanarwa da suka fitar da ke cewa ci gaba da tsare Badejo da jami'an tsaro ke yi bayan kwanaki 10 da kama shi, na nuni da cewa gwamnati ba ta da niyar gurfanar da shi a gaban kuliya a nan kusa.
Sanarwar wacce ta fito ta hannun Ambasada Mohammed Tasi'u Suleiman, ta ce rundunar sojoji Najeriya da aka ce su ne suka kama Badejo ba ta da hurumin tsare duk wani mutum fiye da sa'o'i 24.
Kungiyoyin sun yi kira ga Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya sa baki tare da ba da umurnin a gaggauta sakin shugaban kungiyar makiyayan.
Abdulkarim Bayero yana daya daga cikin shugabanin matasa na kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, ya kuma ce Fulani da aka tuntuba suna goyon bayan wannan kungiyar sa-kai da Badejo ya kafa, domin ya taimaka wajen kawar da zargin da ake yi wa Fulani makiyaya, kuma kungiyar za ta yi aiki kafada da kafada da jami'an tsaro a yankin da suke.
Shi kuwa shugaban Kungiyar Fulani Cattle Breeders MACBAN Alhaji Usman Ngenzarma ya ce, kungiyoyi irin nasu suna da hurumin kafa kungiyoyi amma fa sai sun hada da samun izini wuri gwamnatin jiha ko na tarayya idan bukatar hakan ta taso.
Ngenzarma ya ce ya kamata a yi la'akari da yawan kiraye-kiraye da ake yi a fannoni daban-daban na kasar kan a kafa ‘yan sandan jihohi domin a taimaka wajen shawo kan rashin tsaro da ya addabi kasar, kuma wannan kira ne mai kyau.
Amma ga kwararre a fanin tsaro, Dokta Yahuza Ahmed Getso, yana ganin akwai abin dubawa a matakan da Badejo ya dauka wajen kirkirar kungiyar sa-kai da ya yi.
Getso ya ce ya kamata Badejo ya tuntubi sauran kungiyoyin Fulani, sannan kuma ya kamata a ce wata hadaka ce aka samu tsakanin kungiyoyin sa-kai da su kungiyoyin Fulani a karkashin jagoranci na tsarin tsaro na jihar.
Getso ya kara da cewa a matsayinsa na shugaban na kasa da ya ce kungiyar na Fulani zalla ne, ya kamata a ce ya sanar da hukumomin tsaro a matakin kasa wadanda za su iya tunanin cewa mene ne dalilin da ya sa za’a kafa irin wannan kungiyar ta sa-kai kafin ya kaddamar da kungiyar.
Tuni gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya musanta cewa yana da hannu wajen kafa kungiyar ‘yan banga da Abdullahi Bello Badejo ya kaddamar a jihar Nasarawa kwanan nan.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna