Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Fararen Hula Akan Zargin Kudaden Yan Gudun Hijira


Gamayyar kungiyoyin ci gaban al’uma dake rajin sake gina yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, sun yi kira ga hukumomin yaki da almundahanar kudaden Jama’a na EFCC da ICPC su kaddamar da bincike kan zargin ofishin sakataren gwamnatin tarayya da badda sawun Naira Biliyan Daya da Miliyan Dari Uku kudaden tallafawa ‘yan gudun hijira da kuma aikin sake gina yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da mayakan Boko Haram suka daidaita.

A wani taron manema labarai a Kano gamayyar kungiyoyin sun yaba da yunkurin Majalisar Dattawan Najeriya game da batun rashawa da karkatar da akalar kudaden tallafawa ‘yan gudun hijira da sake gina yankin Arewa maso Gabashin kasar, amma kuma sun bukaci hukumomin EFCC da ICPC da su kaddamar da bincike game da wannan zargi.

Kakakin gamayyar kungiyoyin Kwamred Kabiru Sa’idu Dakata, yace bisa bincikar zargin da Majalisar Dattawa tayiwa babban sakataren gwamnatin tarayya bisa yadda ya jagoranci wasu ayyuka a yankin Arewa maso Gabas. Haka kuma anyi zargin cewa an bayar da kwangilolin ne ga abokansa da kuma ‘yan uwan sakataren, da kuma cewa anfitar da kudade ba ranar aiki ba.

Sai dai Kwamrad Kabiru Dakata yace muddin hukumin biyu sukayi buris da wannan kira kwatankwacin yadda sukayi game da zargin akan babban hafsan mayakan Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai, babu shakka kungiyoyin ba zasu nade hannunsu ba.

Tuni dai Majalisar Dattawa ta kafa wani kwamitin bincike game da wannan batu karkashn kulawar Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna.

Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

XS
SM
MD
LG