Kungiyoyin sa kai na farar hula guda 18 sun baiwa Gwamnatin Jihar Zamfara wa'adin sa'o'i 48 da ta saki shugabannin 'yan majalisar dokokin jihar dake tsare yanzu haka a hannun hukumar tsaro ta cikin gida DSS.
Sunce idan ba ayi hakan ba kuma za su yi shirin babbar zanga-zangar nuna rashin amincewarsu.
Shugaban Majalisar Matasan Arewa reshen Zamfara, Manir Kaura, wanda shi kuma yake jogorantar hadakar kungiyoyin yace, baza su yarda da wannan ba.
Ya kara da cewa wannan cin zarafin gwamnatin dimokradiyya ne don bisa ka'ida da tsarin mulkin kasar ya shimfida suna da damar gabatar da hujjojin su akan duk abin da suke so.
Sai dai kuma kwanakin baya wasu matasa sun fito suna kushe yunkurin da aka ce 'yan majalisar ke yi na tsige Gwamna Abdulaziz Yari.
Domin karin bayani, saurari cikakke rohoton Murtala Faruk Sanyinna.