Kungiyar Chelsea ta Ingila, da Bayern Munich ta kasar Jamus da Napoli ta kasar Italiya, na daga cikin kungiyoyin da suka kasa suka tsare don yin zawarcin dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo.
A karshen makon da ya gabata, Ronaldo, dan shekara 37, ya fadawa United cewa su ba shi damar ya tafi in har an samu tayi mai tsoka yayin da ake cin kasuwar ‘yan wasa kamar yadda AP ya ruwaito.
Shi dai Ronaldo dan asalin kasar Portugal, na da burin ganin yana buga wasa a gasar Champions League.
Ya kasance dan wasa da ya fi zura yawan kwallaye a kungiyar ta United a kakar wasan da ta gabata, inda ya ci kwallo 24.
Sai dai kungiyar ta Red Devil ta kare a matsayi na 6 a teburin gasar ta Premier League a kakar wasan da ta wuce.
A bara Ronaldo ya koma Old Trafford bayan ya baro Juventus, a halin yanzu kuma yana da ragowar shekara daya a kwantiraginsa da United.
Kamfanin dillancin labarai na PA ya tuntubi wakilin Ronaldo da na United kan wannan batu.