A daidai lokacin da gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce ta soke tsarin kiwon dabobbi na zamani, wanda aka fi sani da Rugga, gamaiyar Kungiyoyin Arewa na ba shugaba Mohammadu Buhari wa'adin kwanaki 30.
Wa'adin kwanaki 30 da suka baiwa shugaba Mohammadu Buhari, na gyara al'amarin Rugga saboda a samu daidaito da gwamnatocin jihohi, a samu zaman lafiya.
Mai magana da yawun gamaiyar kungiyoyin Arewa Sheriff Nastura Ashir, ya shawarci gwamnatin taraiyya da ta yi watsi da adawar da wasu shugabannin ke yi akan shirin Rugga, domin a cewar sa ba zai haifar da alheri ba. Ya ce suna goyon bayan a sake tsarin kasar idan yin haka zai sa a zauna lafiya.
Akan ko a yi Rugga ko a soke, Sheriff ya ce an sa siyasa da addini ne a cikin al'amarin, saboda haka a yi kokarin yin sulhu tsakanin gwamnoni, don sune suka fara wannan maganar ta yin filayen kiwo.
Akan mayar da martani ga 'ya'yan kungiyar, babban lauyan Femi Falana yace ba dole ba ne jihohi su yi filayen kiwo, sai in sun ga dama, kuma asali ma shugaba Buhari, ba shi da iko kan filaye a jihohi sai dai a babban birnin tarayya Abuja inda yake da iko.
Femi Falana ya kara da cewa a Jamhuriya ta farko anyi filayen kiwo kuma gwamnatin lokacin ta yi ne a jihar Cross Rivers.
Abin jira a gani shi ne matakin da kungiyoyin zasu dauka a karshen wa'adin kwanaki 30 da suka bayar.
Medina Dauda ta aiko da wannan rahoton daga Abuja.
Facebook Forum