Jihar Kaduna kamar wasu jihohi da suke arewacin Najeriya suna ganin kwarar 'yan gudun hijira daga jihohi da suke arewa maso gabashin kasar, musamman Barno, da Yobe da Adamawa.
Wadannan jihohi suna fuskantar ci gaba da tashe tashen hankula sakamakon tada kayar baya daga 'yan kungiyar Boko Haram.
Wadanda suka zanta da wakilin Sashen Hausa Nasiru Birnin Yero, sun ce a rayuwarsu basu taba fuskanta mawuyacin hali irin wannan ba. Wata daga Izge Mama Hadiza, tace babu abinci babu na sha, kuma hatta sana'a idan mutum yace zaiyi babu hali. Tace yanzu dai sun zubawa Allah ido.
Aisha Adamu, daga Gambirun Ngala tace har ciyayi ta ci a lokacinda suke gudun hijira a daji. Inda tayi jinya.
Ga karin bayani.