Sa'o'i sama da 24 bayan da aka kama wani jirgin sama dankare da makamai a filin saukar jiragen sama ta mallam Aminu Kano, kan zargin sauka cikin kasar ba bisa ka'ida ba, har yanzu mahukuntan Najeriya basu ce kala ba kan batun.
Rahotanni daga kano suna cewa an tsare ma'aikatan jirgin turawa su bakwai.
Mazauna yankin suna mamaki da kuma bayyana ra'yoyinsu dangane da wannan batu. Wasu suna cewa akwai buktar Najeriya ta dauki kwararan mataki kan hana aukuwar haka. Suna cewa wannan shine karo na uku da jirage dauke da makamai suke sauka cikin kasar a yanayi mai kamar ta jiyan.
Wani mai fashin baki kan al'amuran yau da kullum Mallam Habu Ahmed ya jefa ayar tambaya, shin me yasa ba'a baiwa jiragen wadataccen mai ne, kuma ganin wannan shine karo na uku da haka yake faruwa, me yasa wannan jirgi baya dauke da takardu da zai gaskanta wannan ciniki ba, kuma me yasa sai a kano suke sauka? Mallam Habu yace idan wannan ciniki na halal ne ai da ya kamata a fito fili a yi bayani.
Ga karin bayani.