Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Sun Himmatu Wajen Kawar Da Matsalolin Da Suka Mamaye Arewacin Najeriya


Matsalolin Arewacin Najeriya
Matsalolin Arewacin Najeriya

Yayin da aka shigo sabuwar shekara ta 2017, batun ilimin ‘ya ‘ya mata da almajirai da kuma dakile yawaitar sake saken aure na daga cikin abubuwan da kungiyoyi da kuma cibiyoyin nazarin ci gaban al’uma sukace zasu sanya a gaba.

Batutuwan ilimi da ilimin ‘yan mata da almajirai da matsalar shaye-shaye da matasa ke yi, na daga cikin manyan matsalolin da suka mamaye lardin Arewacin Najeriya. game haka ne kungiyoyin rajin ci gaban mata da yara kanana, da kuma cibiyoyin nazari da bincike kan harkokin rayuwar iyali ke shan alwashin ribanya kokarinsu wajen cimma muradunsu a wannan shekara ta 2017.

Daraktar cibiyar nazarin jinsin bil Adama da inganta rayuwar iyali ta jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Aisha Abdul Isma’il, tace a bana cibiyar na da tsare-tsaren cimma muhimman muradun da ta saka a gaba. Ta kara da cewa la’akari da yawa da kuma nauyin aiyukan da suka rataya a wuyan cibiyar, ya sanya take kokarin kulla kawance da sauran hukumomi da cibiyoyi don cimma nasara.

A shekarar da ta gabata ne aka gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki kan kalubalen cin zarafin kananan yara da mata, wadda cibiyar bincike kan lamuran dimokaradiyya ta Mambayya a jihar Kano ta shirya.

Malama Hauwa Ibrahim El-Yakubu, guda cikin wakilan da suka halarci taron tace a wannan shekara ta 2017 hukumomi da kungiyoyi ya kamata su himmatu wajen aiwatar da abubuwan da taron ya cimma.

Domin karin bayani ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG