Shugaban tawagar kungiyar Tarayyar Tarai Mr. Kurt Cornelis yace wannan shiri na jihar Borno ne kawai kuma an kirkiro shi ne don taimakawa al’ummar jihar wurin samar da abubuwar more rayuwa ga mutanen da wannan rikin ya shafa don su ci gaba da gudanar da rayuwarsu.
Mr. Cornelis ya kara da cewa wannan shirin shekaru uku zai taimakawa gwamnatin jihar Borno, saboda EU ba zata iya ci gaba da bada taimako na tsawon loakci ba. Ya amsa tambaya a kan rashin tsaro da ake fama da shi a wasu yankuna da yanda zai shafi shirin nasu, inda ya kyautata zaton cewa akwai abubuwan da zau iya yi su kula da yanda suke gudanar da ayyukansu.
Anasa bangare, mataimakin Gwamnan jihar Borno Usman Durkwa da ya wakilci Gwamnan jihar Kashim Shattima yace matsalar rikicin Boko Haram ya shafi shiyar Arewa maso gabashin Najeriya kuma an yi asara kusan biliyan tara amma an samu mafi yawan asarar ne a jihar Borno. Mataimakin gwamnan ya lissafto adadin asarar rayuka da na dukiyoyi da aka yi a jihar.
Ga rahoton wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Haruna Dauda da Maduguri:
Facebook Forum