Taken da AU ta bai wa ranar ta bana shine lokaci ya yi da kowane yaro ‘dan Afrika zai samu ilimin zamani, dalilin da kenan a Nijar masu kare hakkin yara ke ganin bukatar amfani da wannan dama don magance tazarar da ake fama da ita a tsakanin yaran karkara da na birane a wannan lokaci da kasar ke ikirarin rungumar wata sabuwar tafiya.
Ranar yaran Afrika wacce ta samo asali daga gwagwarmayar neman ‘yancin samun dadaito a tsakanin al’ummar Afrika ta Kudu a zamanin gwamnatin wariyar launin fatar kasar musamman yadda aka kafa shingen da ya hana ‘ya'yan bakaken fata sukunin shiga makarantun da ake dauka a matsayin na masu galihu.
Lokaci ne da kuma kungiyar hadin kan kasashen Afrika AU ke amfani da shi don fadakarwa kan mahimmancin shimfida adalci a tsakanin jama’a.
A wannan karon, kungiyar AU ta kudiri aniyar bai wa kowane yaro damar samun ilimi daidai da sauran abokansa.
Kumgiyar ta kuma bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen fifita wasu yara kan wasu akan sha'anin ilimi. Matakin da shugaban kungiyar ALTEN mai yaki da bautar da yara Mohamed Moussa ya bayyana gamsuwa da shi.
Wadanan ‘yan fafutuka na ganin faduwa ta zo daidai da zama ne a bisa la’akari da yadda kudirin na kungiyar tarayyar Afrika ke zuwa a wani lokacin da sabbin hukumomin Nijar suka ayyana shirin aiwatar da sauye sauye a illahirin fannonin da ke da nasaba da harkokin tafiyar da lamuran kasa.
Fannin ilimi da kyautata ‘yancin yara na daga cikin wadanda ya kamata a bai wa fifiko inji su.
Asusun MDD mai kula da tallafa wa yara UNICEF ya sanar cewa har yanzu gwamnatoci a kasashen Afrika ba sa kashe kudaden da suka dace da tsarin bada ilimi mai inganci ga yaran nahiyar.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna