KANO, NIGERIA - Wata kididdiga da ofishin shiyyar Kano na hukumar NAPTIP mai yaki da fataucin bil’adama ta Najeriya, wadda ta kunshi jihohin Kano, Kaduna, Katshina, Jigawa da jihar Bauchi, ta nuna daga watan Janairu zuwa makon jiya, Jami’an shiyyar sun yi nasarar ceto samari da ‘yam mata fiye da 160 daga hannun miyagun mutanen da ke safarar ‘yan Najeriya zuwa kasashen Libya da Italiya.
Bayanai sun fayyace cewa, matasan da galibin su sun fito daga shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, Jami’an na hukumar NAPTIP na samun kubutar dasu ne bisa tallafin jandarmomin jamhuriyar Nijar akan iyakokin kasashen biyu.
Hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da hukumar ta NAPTIP ke fama da kalubalen kudade dana kayayyakin aiki.
Amma, sai dai, kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida wadanda ke aikace aikacen yaki da cin zarafin bil’adama da kuma safara da fataucin mutane sun ce sakaci da rashin kulawar gwamnati ne ya sanya batun yaki da masu safarar ‘yan kasa ke samun koma baya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari: