An gudanar da taron addu'o'i ne a babban Masallacin Juma’a dake birnin Yamai, da hantsi inda daruruwan mutane masu nakasa suka hallara domin gudanar da addu'o’in zaman lafiya.
A lokacin da kasar ta shiga yanayin da ake cigaba da jiran sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 13 ga watan Disamba, wanda ke dai-dai da lokaci da ya rage kwanaki 10 a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin kasa da na shugaban kasa.
Shugaban kungiyar addinin Islama ta AIN Cheik Djibril Soumaila Karanta shine ya jaogranci wadanan addu’oi. Inda ya ce "Ya Allah kai ka yi alkawalin duk wani bawan ka da ka dauke mishi gani, kuma ya hakura, kana jin kunyar ya sake rokon ka baka amsa masaba. Don haka Allah gamu munzo muna rokon ka kai ne mai yi, mai kowa mai komai, Ya Allah ka duba mu da idon rahama ka bamu kwanciyar hankali, ga mu zamu shiga zabe Allah ka zaba muna wadanda suka fi zama alkhairi."
Shuwagabanin kungiyoyin nakasassu sun yi amfani da wannan damar domin jan hankulan ‘yan siyasa. Malan Habibou Abdoulaye shine jagoran hadakar nakasassun yankin Yamai. Yana mai cewa "Kiran mu ga shugabanin masu zuwa shine, kada ace ana yaki da mabarata, su sani cewar muma muna bada gudunmawa lokacin zabe, don haka akwai bukatar a duba wadannan mutanen, suna da nasu bukatocin, don haka akwai bukatar a tallafa musu."
Alkaluman kididigar al’umar Nijar na shekarar 2012 sun yi nuni da cewa yawan mutane masu bukata ta musamman a kasar ya haura 700,000 saboda haka jama’ar nakasassu na da mahimanci a zabe.
Bayanai na nunin a zaben na wannan karon yawan ‘yan takara masu nakasa ya zarce wadanda aka saba gani a zabubukan da suka gabata, galibinsu masu neman kujerar wakilci a majalisun kananan hukumomi.
Ga rahoton wakilin muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma a cikin sauti.