Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Musulmi A Lagos Tace Obasanjo Ya Bar Jaki Yana Bugun Taiki


Tsohon Shugaban Najeriya, Dr.Olusegun Obasanjo,
Tsohon Shugaban Najeriya, Dr.Olusegun Obasanjo,

Yan Najeriya suna ci gaba da maida martani dangane da wasikar da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaba Muhammadu Buhari. Kamar sauran bangarorin kasar, al’ummar yankin kudancin Najeriya suma sun maida martani inda wadansu suka goyi baya, wasu kuma suke kushewa tsohon shugaban kasar.

A cikin sanarwar da ta fitar, wata kungiya a birnin Ikko mai suna “The Muslim Right Concern” ta soki tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo tare da bayyana cewa, ya bar jaki yana dukan taiki. Bisa ga cewar kungiyar, kamata ya yi tsohon shugaban kasar ya dora tsaiko da kuma tafiyar hawainiya da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke yi a kan ‘yan majalisar tarayya wadanda kungiyar tace suna watsi da duk wani shirin gina kasa da shugaba Muhammadu Buhari ke gabatar masu.

Shugaban kungiyar Professa Ishak Akintola yace kungiyarsu bata goyon bayan wannan matsayi na Dr Olusegun Obasanjo, kuma tana kira gareshi da ya janye wannan wasika da ya rubuta, tare da yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da wannan wasika. Ya kuma tsaya takarar neman shugabanci a zaben da za’a a gudanar a shekara ta dubu biyu da goma sha tara.

Yace, “A ganinmu shugaba Muhammadu Buhari ya taka rawar gani in banda tarko da ‘yan majalisa ke kafa masa da tuni ya wuce nan, don haka akwai bukatar Buhari ya yi tazarce, domin kuwa sai ya sake dawowa ne zai sami ‘yan majalisa na kwarai da zasu taimaka masa wajen tafiyar da kasa kamar yadda ‘yan Najeriya ke fata.”

Akasarin magoya bayan Muhammadu Buhari da Sashen Hausa ya zanta da su a birnin Ikko, sun dora laifin gazawar Muhammadu Buhari kan ‘yan majalisun tarayya da na dattijai, da kuma na wakilai, wadanda akasarinsu ‘yan jam’iyar PDP ne suka sauya sheka ana dab da gudanar da zabe, wanda kuma har yanzu ana ganin angulu da kan zabo ne suka yiwa jam’iyar ta APC.

Wani mai sharhi kan lamura, Alhaji Ado Dansudu ya bayyana cewa, ko ba komi, shugaba Muhammadu Buhari ya tsufa saboda haka kamata ya yi ya zama uban kasa ya koma gefe ya sa ido, inda yaga ana bukatar gyara yace a gyara.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Babangida Jibril ya aiko mana daga Ikko.

Martani daga Ikko-3:04"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG