Gwamnan jahar Ekiti ta Kudu maso yammacin Najeriya, Ayodele Fayose ya ce da yadda Allah sai ya kara da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019. Ya ce Najeriya fa na bukatar Shugaban kasa na gari; gashi kuma shi mutum ne mai kuzari da kyau kuma zai iya hada kan kasa. Ya ce duk mai shakka ya rubuta ya ajiye – sai ya kayar da Buhari a arewa da ma Najeriyar baki daya.
Da aka tambaye shi ko bai ganin kasancewar jam’iyyarsu ta PDP za ta zabi dan takara hakan zai shafi sha’awarsa ta yin takara, sai y ace ai kundin tsarin mulkin Najeriya y aba shi damar tsayawa takara kuma zai iya amfani da wannan damar. Ya ba da misalin yadda marigayi Alhaji Abubakar Rimi daga arewa ya tsaya takara koma bayanda aka tsayar da Mista Olusegun Obasanjo daga Kudu; Peter Odili daga Kudu maso kudu ya tsaya ko ma bayan tsayar da marigayi Musa ‘Yar’Aduwa a arewa.
Mista Fayose ya ce ai babu wata matsala, idan ya fadi sai kawai ya koma gidansa ya huta. Ya ce komai nufin Allah ne – kama daga yin takarar da kuma yin nasara ko akasin hakan. Ya ce, don haka, idan Allah bai nufe shi da yin takara ba ba zai yi ba, zai bi wanda dan jam’iyyarsu ta zaba to amma haka kawai ba zai yanke kauna ya sallamar ba.
Ga wakilinmu Hassan Umar Tambuwal da cikakken rahoton:
Facebook Forum