Shugaban kungiyar na jihar Oyo Alhaji Yakubu Ganyo shine ya fadi a ganawar da yayi da Muryar Amurka. “Mun yi Allah wadai ga abunda yake faruwa ga ‘yan uwanmu makiyaya, da ake kashe su kowani lokaci.”
Shugaban ya kara da cewa “Wallahi gwamnati tazo ta dauki mataki, yanda ya kamata don Fulani sun gaji. Ana kashe mu babu dalili, kuma gwamnati bata dauki mataki ba.”
Wadannan yara dai an kashe su ne a Karamar Hukumar Atisbo a jihar Oyo.