WASHINGTON, DC —
Rikicin cikin gida kan shugabancin majalisar dokokin jihar Kaduna ya yi sanadiyar dakatar da tsohon shugaban marasa rinjaye Alhaji Shehu Usman Dan Fulani har na tsawon watanni shida.
Dakatarwar ta biyo bayan rahoton kwamitin da majalisar ta kafa domin binciken zargin da Alhaji Shehu Usman ya yi inda ya ce gwamnatin jihar ta baiwa kowane dan majalisar nera miliyan goma goma da suka tsige tsofofin shugabannin majalisar a matsayin toshiyar baki. Mr. Philemon Usman na Gidan Mana shi ne shugaban kwamitin da ya bayar da shawarar dakatar da tsohon shugaban marasa rijayen.
A bayanin da ya yi Philemon Usman ya ce idan ba'a manta ba ya ce shi tsohon kakakin majalisar ya jagoranci tawagarsa suka je ofishin 'yan jarida inda suka gabatar da bayyanai. A cikin bayanan shi Dr. Shehu Usman Adamu ya fito karara a gidan telibijan na AIT cewa duk wadanda suka shiga cikin tsarin neman canjin shugabanci an basu kudi nera miliyan goma kowanensu saboda su yi aikin. Philemon ya ce babu wanda aka bashi ko kwandala don haka tamkar zagi aka yi masu. Ya ce to idan basu fito sun dauki mataki ba jama'a zasu gani kaman bayanin da ya yi gaskiya ne.
An tambayi Philemon Usman ko kwamiti dinsu ya tantance abubuwan da aka fada. Ya ce sun je telibijan na AIT inda aka basu bidiyon maganar da ya yi. Da suka tara bayyanan sun gayyaci Shehu Usman har sau hudu domin ya bayyana gaban kwamitin ya kare kansa. Sai dai a kowane lokaci aka kirasa sai ya bada wasu hujjoji da basu da tushe bare matsayi. Duk wani 'yanci da yake da shi na kare kansa ko kwato kansa kusan ya kawar dasu domin kin bayyana a gaban kwamitin na binceken lamarin. Wato ya ba kwamiti dama da yanke hukunci bisa ga abun da ya gani ya yi daidai.Ya ce sun yi anfani da dama da suke dashi na ladabtar da duk wani dan majalisa da ya yi abun da ba daidai ba.
Kan ko wasu kalamu da ya yi da can cewa aikin da gwamnan jihar ya yi cikin kasafin kudin bana bai taka kara ya karya ba shi ne musabbabin ladabtar da shi,sai Philemon Usman ya ce babu ruwansu da abun dake tafiya a gari. Akasarin gaskiya ma shi bai san ya yi wadannan kalamun ba.
Amma Alhaji Shehu Usman Dan Fulani wanda aka dakatar ya ce majalisar bata yi masa adalci ba. Ya ce kwamitin ya rubuto mashi har sau hudu kuma yana bada amsa na neman a yi gyara kafin ya bayyana a gabansa domin kwamitin ba'a kafa shi yadda dokar majalisa ta tanada ba. Ko a majalisar ma wasu sun fada haka cewa kwamitin ba'a kafa shi ta hanyar da ta dace ba. Amma tun da wannan lamarin ya faru zasu zauna suga matakin da ya kamata su dauka domin tun watan Satumbar bara majalisar ta rabu gida biyu.
Ga karin bayani.