Kungiyar Islaman nan mai tsatstauran ra’ayi a arewacin Najeriya tace zata ci gaba da kai hare hare a yankin sai gwamnati ta cika tsauraran sharudan da ta gindaya. A cikin sanarwar da ta bayar, kungiyar Boko Haram ta jajada cewa, tilas ne a kafa shari’ar Islama a dukan arewacin Najeriya kuma gwamnatin jihar Borno tayi murabus. Kungiyar kuma tana so a saki dukan membobinta da ake tsare da su a kuma tuhumi tsohon gwamnan jihar Borno da manyan jami’an tsaro sabili da kashe shugaban kungiyar. Kungiyar Boko Haram ta bada wannan sanarwar ne yau Litinin a Maiduguri babban birnin jihar Borno. Sun ba wasikar kan magana, “Sharuddan tattaunawa da shugaba Goodluck Jonathan da gwamna Kashim Shettima". Shettima, sabon gwamnan jihar Borno ya bayyana cewa, a shirye yake ya tattauna da Boko Haram. Makon jiya shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana goyon bayan tattaunawa da kungiyar mayakan.
Kungiyar Islaman nan mai tsatstauran ra’ayi a arewacin Najeriya tace zata ci gaba da kai hare hare a yankin sai gwamnati ta cika tsauraran sharudan da ta gindaya.