Katafaren kamfanin man fetur din nan na Royal Dutch Shell, yace ba zai iya cika wasu daga cikin alkawuran da ya dauka cikin gwangilolinsa ba, saboda yawan lahanin da ake wa manyan bututan mai a Nijeriya.
Kamfanin y ace masu bincike sun gano cewa akwai yanka a bututansa da suka ratsa yankunan Niger-Delta, wanda hakan ke nuna cewa barayi ne da ke kokarin tatsar man su ka lalata bututan.
Kamfanin na Shell y ace saboda yawan huje-huje jikin batutansa, ranar Litini reshen kamfanin na Nijeriya ya yi shelar samun nakasu a ayyukansa. Wannan shelar dai a dokance ta halalta wa kamfanin na Shell dakatar da aiwatar da yarjajjeniyar kwantaragi, saboda matsalolin sun sha karfinta.
Wannan shelar ta shafi jigilar danyan mai daga yankin Niger-Delta mai arzikin man fetur cikin watan Yuni da Yuli.
A watan mayun 2010 sai da kamfanin na Shell ya dakatar da sarrafa danyen mai na tsawon watanni biyu saboda wutar da ta kama bututan manta. Kamfanin y ace barayi ne su ka haddasa wutar.