A cigaba da fafatawa da akeyi a gasar cin kofin duniya, ajin Mata na shekarar 2019 a can kasar Faransa.
Tawagar kungiyar kwallon kafar Mata ta kasar Amurka ta kafa tarihi a gasar cin kofin kwallon kafa ta Mata, bayan da ta lallasa takwararta ta Thailand da kwallaye 13-0 a ranar Talata 11 ga watan Yuni 2019 a matakin wasan rukuni.
Matan Amurka sun fara jefa kwallon sune a mintuna na sha biyu da fara wasan, 'yar wasan su mai suna Alex Morgan inda aka tafi hutun rabin lokaci 3-0.
Bayan dawowa daga hutun ne Amurka ta zurara kwallaye 10, jimmilar kwallaye sha uku inda 'yar wasan Alex Morgan ta jefa shida daga ciki.
Tawagar ta Matan Amurka a yanzu ba wata kungiyar da takaita zura kwallaye a raga cikin wasa guda a tarihin wasan gaba daya, bayan da ta karya tarihin kasar Jamus wadda a shekarar 2017 ta lallasa Ajantina daci 11-0.
Bayan tashi daga wasan kocin kungiyar Jill Ellis ta bayyana murnarta inda ta zubar da hawayenta, saboda tsabar murnar ganin ta kafa wani sabon babi na tarihi a duniyar wasanni.
Kasar Amurka tana mataki na daya a rukunin wasan zagaye na farko da maki 3, kwallaye 13, ranar Lahadi mai zuwa zasu fafata da kasar Chile a wasan zagaye na biyu cikin rukuni.
Facebook Forum