Hadakar kungiyar malaman jami’o’in Najeriyan ASSU, reshen jihar Taraba ta bayyana kaduwarta game da halin da wadanda ke gudun hijira na yankin Lau ke ciki ,lamarin da suka ce ya kamata gwamnatin jihar Taraban ta tashi tsaye.
Dr Ruben Jonathan dake zama shugaban kungiyar malaman ta reshen jihar Taraba ya bayyana yadda aka yi,har suka sami labarin halin da wadannan mutane ke ciki.
Alhaji Muhammad Bakari Katibu da sauran yan gudun hijiran da suka baro gidajensu a yankin Katibu duk sun bayyana farin cikinsu game da taimakon da suka samu daga kungiyar Malaman.
Baya ma ga al’umman Katibu,haka nan kuma kungiyar Malaman ta bada irin wannan tallafi ga wasu al’ummomin da lamarin ya shafa na yankin Lau din.
Kamar dai yadda alkalumma ke nunawa,daruruwan jama’a ne dai suka rasa muhallansu sakamakon harin kabilancin da aka kai musu a yankunan Katibu,Baba-Gasa da wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Lau,dake cikin jihar Taraban a kwanaki lamarin da ake dangatawa da fadan manoma da makiyaya,kuma akasarin maharan sun fito ne daga jihar Adamawa dake makwabtaka da jihar Taraba,koda yake kawo yanzu lamurra sun kwanta a wadannan yankuna.
A saurari karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz
Facebook Forum