Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kodagon Najeriya tayi barazanar shiga yajin aiki


NLC (file photo)
NLC (file photo)

Ma’aikata a wadansu daga cikin manyan kungiyoyin kodagon Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki muddar gwamnati bata aiwatar da yarjejeniyar kara masu albashi da aka cimma bara ba.

Ma’aikata a wadansu daga cikin manyan kungiyoyin kodagon Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki muddar gwamnati bata aiwatar da yarjejeniyar kara masu albashi da aka cimma bara ba. Shugaban kungiyar kodago ta Najeriya Abdulwaheed Omar ya ba gwamnati wa’adin ne yau Jumma’a cewa, ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu a shirye suke su shiga yajin aiki cikin makonni biyu idan ba a aiwatar da yarjejeniyar ba. Kungiyar kodago ta Najeriya NLC da kuma gamayyar kungiyoyin kodago da kuma Najeriya tace gwamnati ta kasa aiwatar da dokar da aka sa hannu a kai farkon wannan shekarar da zata kara mafi kankancin albashi zuwa dala dari da ishirin a wata. Kafin sa hannu a wannan sabuwar dokar dai, ana biyan dala hamsin ne a matsayin mafi kankancin albashi. Najeriya ce kasar Afrika da tafi sayar da man fetir a kasashen ketare.

XS
SM
MD
LG