Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Diflomasiyya A Najeriya Sun Yi Tur Da Hare-Hare


Wani dan sanda na magana a waya a lokacin wani harin bam a hedkwatar rundunar 'yan sandan Najeriya a Abuja
Wani dan sanda na magana a waya a lokacin wani harin bam a hedkwatar rundunar 'yan sandan Najeriya a Abuja

Ma'iakatan jakadancin na Turai da Amurka sun ce bai kamata a kyale masu kai hare-haren bam a Najeriya su na cin karensu babu babbaka ba

Jami’an diflomasiyya na Amurka da Turai sun hada kai wajen yin tur da munanan hare-haren da suka kashe mutane 28 cikin wannan makon a yankin arewacin Najeriya.

Jiya litinin, an kashe mutane uku, yayin da wasu akalla uku suka ji rauni a wani hari a garin Maiduguri dake yankin arewa maso gabashin kasar. Kwana guda kafin nan, an kashe mutane 25 a wata mashayar dake garin a wani harin bam din da ake kyautata zaton wasu masu kishin Islama ne suka kai.

A wata sanarwar hadin guiwa da suka bayar yau talata, jami’an jakadancin Kungiyar Tarayyar Turai da na Amurka dake Najeriya, sun yi tur da hare-haren, su na masu fadin cewa babu al’ummar da ta cancanci zama da irin wadannan munanan tashe-tashen hankula, kuma bai kamata a kyale masu aikata wannan abu su na yi duk lokacin da suka ga dama ba.

Ana kyautata zaton hare-haren aikin kungiyar nan ce ta Boko Haram, amma kuma babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai su. Kungiyar ta dauki alhakin kai wani harin dabam a kan hedkwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Abuja cikin wannan watan, kuma an dora mata alhakin hare-hare da dama a kan ‘yan sanda da jami’an gwamnati da kuma shugabannin addini.

Jami’an gwamnatin Najeriya sun yi tayin tattaunawa da wannan kungiya mai gudanar da ayyukanta a asirce, ammam masu magana da yawunta sun ki yarda da wannan tayin.

XS
SM
MD
LG