Kungiyoyin biyu sun gabatar da wannan kiran nasu a wata sanarwar hadin guiwar da suka gabatar ran lahadi inda suke cewa a zaben shakarar 2007, ankashe akalla mutane 300 a tashe-tashen hankulan dake da nasaba da zabe.Sanarwar tana mai cewa ana kyautata ganin dakyar ne idan ba’a sami karuwar tashe-tashen hankula a gabanin zaben da za’a gudanar a watan Afrilu mai zuwa ba. ‘Hukumar kare hakkin BilA dama ta HRW da kungiyar lauyoyin Nigeria suka ce kwamatin gyara kundin tsarin zabe da marigayi shugaba Umaru Musa ‘yar Adu’a ya kafa bayan zaben shekarar 2007, ya gano cewa daga lokacin da Nigeria ta sami ‘yancin kanta a shekarar 1960, ba’a taba samun wani dan Nigeria da aka gurfanar dashi gaban shari’a saboda aikata laifukan da suka jibanci nasaba da rikicin zabe ba, ballantana aga an hukuntasu.
Kungiyar kare ‘yancin Bil Adama ta HRW tayi kiran da a gurfanar da masu tada hargitsin siyasa a gaban shari’a
Kungiyar kare hakkin BilAdama ta HRW da shugaban kungiyar lauyoyin Nigeria sun yikira ga Majalaisar dokokin Nigeria da ta kafa wani kwamatin da zai binciki ha’incin zabe da rikicin zabe, sannan kuma kwamatin ya gurfanar da wadanda suka aikata laifukan zabe a agaban shari’a.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024