Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Alshabab Ta Kai Hari Kan Wani Otel a Magadishu


Akalla mutane tara da suka hada da wani janar na soja sun mutu, wasu 15 kuma suka jikkata a wani harin da kungiyar Alshabab ta kai a wani otal a Moghadishu.  

A jiya Lahadi wata mota dauke da Bam ta tarwatse a kusa da wani Otel a Magadishu, babban birnin kasar Somalia. Bayan tashin bom din, harbe-harbe sun biyo baya a tsakanin ‘yan ta’adan da ‘yan sanda.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Al-shabab ta dauki alhakin kai wannan harin.

Wani taro a kasar Somaliya
Wani taro a kasar Somaliya

Wani da ya shaida lamarin, ya ce bom din ya tashi a jiya Lahadi a kusa da Otel Afrik, yankin mai cike da shingayen bincike na jami’an tsaro akan hanyar zuwa tashar jirgin sama da ke Magadishu.

‘Yan sanda sun tabbatar da cewar ‘yan kungiyar Al-shabab sun abka cikin Otel din, amma sun samu damar kubutar da mutanen da ke ciki, wanda suka hada da tsohon ministan tsaron na Somali Yusuf Siad Inndha-Adde.

Wakilin Muryar Amurka Abdikafi Yusuf Aden, na daya daga cikin wadanda abun ya rutsa da su a cikin Otel din, amma dai ya kubuta.

Qarax Hotel Afrik
Qarax Hotel Afrik

Aden, ya ce bayan tashin bom din hayaki ya turnike, jama’a sun yi ta fadowa daga saman bene, don tsira da rayukansu.

XS
SM
MD
LG