Sai dai bincike ya tabbatar da cewa ta haramtaciyar hanya wadanan makamai ke shiga hannun ‘yan bindiga.
Kungiyar ta Amnesty tace a yayin gudanar da wannan bincike ta nazarci hotuna da bidiyo a kalla 400 wadanda reshen kungiyar IS da kungiyar AQMI suka yada a kafafen sada zumunta da wadanda kungiyoyin sa-kai masu aikin tsaro a kasashen Mali da Burkina Faso suka wallafa a yanar gizo da kuma bayanan da ta tattara sun tabbatar da cewa bindigogin da ke hannun baraden wadanan kungiyoyin daga janerun 2018 zuwa Mayun 2021 kirar kasashen Turai ne musamman samfarin kasar Serbia.
Sakataren kungiyar RJPS mai fafitikar wanzarda zaman lafiya a Nijer Souley Mage Rogeto ya ce ya gamsu da bayanan wannan rahoto.
Kungiyar ta Amnesty tace koda yake sau tari ‘yan ta’adda kan kwashi ganimar makamai a duk lokacin da suka yi katarin samun galaba a gobzawarsu da jami’an tsaro bincike ya gano wasu hanyoyin na daban da bindigogi ke shigo wadanan tsageru.
Yayinda kuma ake ganin yiyuwar wasu jami’an tsaro na saidawa ‘yan ta’adda makamai ko su bayar akan wata manufa.
Ganin yadda manuniya ta fara fayyace ainihin hanyoyin da kungiyoyin ta’addanci ke samun makaman da suke amfani da su wajen farwa jama’ar yankin Sahel Souley Mage na cewa ya zama dole gwamnatocin kasashen da abin ya shafa su bi diddigi.
Kasahen Faransa da Slovakia da jamhuriyar Tchekc na sayarwa kasashen Sahel makamai a hukumance dalili kenan kungiyar Amnesty ta gargadi gwamnatocin wadanan kasashe da takwarorinsu na sahel su tsaurara matakan zuba ido akan yadda ake amfani da irin wadanan makamai koda yake masana na kallon wannan kira tamkar wani yunkurin rufewa kasashen sahel hanyoyin sayen makamai a dai dai lokacin da yaki ke kara kazancewa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: