Dangane da sakin mutanen da aka tauye hakkinsu, gwamnan Bauchin Barrister M.A. Abubakar yace yana tabbatarwa al'ummar Bauchi da ma duniya gaba daya cewa gwamnatinsa tana kan tafarkin tabbatar da 'yancin dan Adam.
Yace duk wata hanyar da za'a bi a tauyewa mutum 'yancinsa gwamnatinsa zata yaketa domin ta kare 'yancinsa.
Bayan shugabannin Amnesty International sun ga gwamnan yace ya bada umurni nan take kwamishanan shari'a ya je ya duba ya kuma saki mutanen su koma gidajensu.
Dr Suleiman Sha'aibu shugaban kungiyar Amnesty International a jihohin arewacin Najeriya ya bayyana makasudin zuwansu gidan gwamnatin jihar Bauchi. Yace sun zo yiwa gwamnan jihar godiya ne a matsayinsu na kasancewa kungiyar dake fafutikan kare hakkin bil Adama. Yace sun nemi hakkin wasu kuma gwamnan da gwamnatinsa sun shiga cikin lamarin kuma an basu abun da suka roka. Wadanda aka tauye masu hakkinsu an sakesu.
Yace ya shiga gidan yarin ya kuma ga yanayin da mutane suke ciki kuma sun shaidawa gwamnan.
Wani dan kasuwa da ya kwashe kwanaki hamsin da ukku a kurkuku da ya samu kubuta ya yiwa Muryar Amurka bayanin yadda lamarin ya faru. Yace katifu aka zo saya a shagonsu bayan sun yi ciniki sai daya daga cikin mutanen yace ya aikata ba daidai ya bisu zuwa caji ofis. Maganar kamar almara haka ya shafe kwanaki 53 kafin ya samu kubuta.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.