A mayar da martani dan majalisar tarayya mai wakiltar Misau da Dan Bam Malam Ahmed Yarima yace yana hawar irin motar da gwamnan ke hawa yanzu tun kafin ya zama gwamna, ma'ana yana da arzikinsa tun kafin ya je majalisar tarayya.
Malam Yarima ya kara da cewa duk inda ya je a duniyar nan yana da gida na kashinkansa, wato tun ba yau ba gizo ke saka. Malam Yarima yace ya taba ware kudi ya taimaki mutane wajen dubu daya da dari shida a matsayin tallafi domin samun aikin yi. Yace ya kuma taimaki dalibai dari biyu da sittin wadanda suke jami'a da politeknic wadanda suke rubuta project na kammala karatu.
Bugu da kari, inji Malama Yarima Yakubu Dogara, kakakin majalisar tarayya ya taimaki gwamnan da kudin neman zabe. Yarima yace ya taimaki 'yan takarar zabuka daban daban da kudade. Shi gwamnan bai kashe komi ba fiye da nera dubu dari hudu.
Amma kwamred Sabo Muhammad kakakin gwamnan yayi bayanai filla filla game da wurin da 'yan majalisun suka yi mitin da gwamna inda suka bayyana irin abubuwan da suke so gwamnan ya basu ko yayi masu.
Sabo Muhammad ya tunashe da Malam Yarima kan taron da suka yi a gidan gwamnatin Kano da ya kunshi su 'yan majalisar wakilan Najeriya daga Bauchi 12 da sanatoci ukku da gwamnan jihar da mataimakinsa da shugaban jam'iyyar APC na reshen jiharsu, wato Uba Ahmed Nana.
A taron ne suka fitarwa gwamnan Bauchin bukatunsu wadanda gwamnan yace ba zasu yiwu ba saboda yin hakan tamkar cin amanar mutanen jihar Bauchi ne. Yace shi Ahmed Yarima ya kawo misali da gwamnatin Isa Yuguda wadda ya yiwa aiki yace a lokacin gwamna Isa Yuguda yana yi masu hakan, wato yana ware masu kudade.
Kakakin gwamnan yace abun da al'ummar Bauchi ke nema a wurin 'yan majalisun tarayya shi ne su fito su bayyana abun da su keyi da nera miliyan 28 da kowane sanata ke samu kowane wata ukku da sunan raya mazabunsu. Haka ma kowane dan majalisar wakilai yana samun nera miliyan 18 kowane wata ukku.
Baicin wadannan kudaden daya daga cikin wakilan, Abdulmummuni Jibrin, ya fito ya fasa kwai inda yace kowane wata dan majalisa baya gaza samun abun da ya wuce nera miliyan ishirin.
Ga rahoton Abdulwahab da karin bayani.